An kashe akalla mutane 10 a yankin Kashmir

Sojin Pakistan
Image caption An bada rahotan cewa 'yan bindigar biyu sun rasa rayukansu

Wasu 'yan bindiga a yankin Kashmir sun kaddamar abinda yai kama da shiryayyun hare hare inda aka kashe mutane akalla 10.

Jami'ai sun ce akalla 'yan bindiga uku sanye da kayan soji ne da farko suka budewa wani ofishin 'yan sanda wuta a lardin Kathua kusa da iyaka da Pakistan, inda suka kashe 'yan sanda biyu da fararen hula biyu.

Daga nan sai suka kwace wata babbar mota, suka kashe direban ta, sannan suka kaiwa wani sansanin soji hari, nanma suka kashe sojoji da dama da suka hada da wani babban jam'in sojin Kasar.

An bada rahotan cewa 'yan bindigar biyu sun rasa rayukansu a musayar wutar.

Harin na zuwa ne kwana uku kachal kafin a soma wani taro da aka shirya tsakanin Fira Ministan India da kuma na Pakistan.

Karin bayani