Ana cigaba da bincike a Kenya

Wasu da suka rasa danginsu a Kenya
Image caption Mutane 61 ne aka tabbatar sun mutu a harin

Ministan cikin gida na Kenya, ya ce kwararrun masu bincike suna cigaba yin gwaje-gwaje a cikin cibiyar kasuwancin nan da masu fafitika na Al Shabab suka kai wa hari.

Joesph Ole Lenku ya ce, kwarraru na Kenya da takwarorinsu daga Amurka, da Canada da Isra'ila da kuma Birtaniya suna binciken kwayoyin halitta da kuma kokarin gano nau'in makaman da aka yi amfani da suk wajen kai harin.

Ministan ya kuma ce, zuwa yanzu gawarwakin da suka rage a cikin cibiyar kasuwancin ba su da yawa.

Akwai kuma wasu gawarwakin wadanda suka mutu sakamakon ruftawar hawa uku na ginin.

Tun farko gwamnatin kasar ta Kenya ta ayyana zaman makokin kwanaki uku domin alhinin rashin mutanen da harin masu kaifin kishin Islama ya rutsa da su a cibiyar kasuwanci ta Westgate dake birnin Nairobi.

Hukumomin kasar ta Kenya sun ce, mutane sittin da bakwai ne suka mutu, sai dai kuma akwai wasu mutanen da har yanzu ba a kai gano su ba.

Amma kungiyar Al Shabaab da ta kai harin tace, mutane dari da talatin da uku ne suka mutu, sai dai ba tantance hakan ba.

Karin bayani