Tasirin Twitter a harin Kenya

Image caption Gwamnatin Kenya da kungiyar al-Shabab sun fahimci muhimmancin Twitter shi ya sa suka mayar da hankali akansa yayin da aka kai harin.

A yayin da hankalin duniya ya karkata ga harin da aka kai a rukunin kantunan Westgate da ke Nairobi, babban birnin Kenya, hukumomin kasar da kungiyar 'yan bindiga ta al-Shabab sun yi ta kokarin watsa sakonninsu game da harin ta hanyoyin sada zumunta.

Ko da gabanin harin da aka kai a Westgate, kungiyar al-Shabab ta yi ta kokarin yin amfani da Twitter da harshen Ingilishi domin watsa al'amuranta ga duniya.

Sai dai sau biyu masu shafin na Twitter suna kulle shafin Twitter na al-Shabab a cikin watanni tara da suka gabata.

Amma a duk lokacin da aka rufe shafin Twitter na al-Shabab, a kan ga kungiyar ta bude wani shafin da wani suna na daban.

An rika fuskantar matsaloli game da sakonni

A lokacin da aka kai hari a Westgate, al-Shabab ta rika watsa bayanai ta Twitter, tana mai cewa ta kai harin ne domin ramuwar-gayya kan dakarun kasar Kenya, wadanda ta ce sun aikata laifuka a Somalia, sannan ta bayyana cewa ''muna yakar kafiran Kenya ne a gidajensu''.

Sai dai ana cikin haka ne, aka kulle shafin.

Amma daga bisani shafukan Twitter da dama sun bayyana, suna ikirarin cewa al-Shahab ke yin amfani da su, lamarin da ya janyo rudani game da takamaimai wanne shafi ne na kungiyar.

Image caption Sai dai ba a samu daidaito daga ma'aikatu daban-daban na gwamnati game da sakonnin da ake aikewa ba

Su ma jami'an tsaron Kenya sun yi ta aikewa da sakonni ga duniya game da abubuwan da ke faruwa ta shafin tweeter a lokacin harin.

Babban Sifeton 'yan sandan kasar, David Kimaiyo, ya ba da sanarwa lokacin da aka kai harin ranar Asabar cewa 'yan sanda sun yi wa rukunin kantunan kawanya, sannan ya bukaci 'yan kasar da manema labarai da su kauracewa yankin da abin ya faru.

Sai dai duk da cewa an rika bayar da bayanai ta Twitter game da harin, an samu matsaloli dangane da gaskiyar abin da ke faruwa a cikin rukunin kantunan, watakila saboda rashin tsara sakonnin da ake aikewa daga bangarori daban-daban na gwamnatin kasar.

Karin bayani