Ana zargin sojoji da yin fyade a Mali

Image caption Sojan Majalisar Dinkin Duniya a Mali

Majalisar Dinkin Duniya ta amsa cewar sojojin kiyaye zaman lafiya akalla 4 ne keda hannu a yi wa wata mata fyade a Mali cikin makon da ya wuce.

Bayan wani biciken da Majalisar ta yi, an nuna mutanen a matsayin wadanda suke cikin sojojin Chadi 1500 dake aiki a cikin rundunar kiyaye zaman lafiyar ta MINUSMA.

An dai yi amannar matar ta je neman magani ne bayan da aka yi mata fyaden a ranar alhamis din da ta wuce a Gao.

Ba a dai san ko 'Yan Chadi na wa ne keda hannu a al'amarin ba, to amma matar da nuna sojoji 4 sun yi mata fyade a wani masauki dake hade da wani gidan giya.

Karin bayani