Girgizar kasa ta hallaka mutane 330 a Pakistan

Image caption Wani dattijo da gidansa ya ruguje sakamakon girgizar kasa

Mutane fiye da 330 sun mutu sakamakon girgizar kasa mai karfin gaske da ta afkawa kudu maso yammacin Pakistan a ranar Talata.

Wasu da dama kuma sun samu raunuka a girgizar kasa a kauyen na Balochistan.

Rahotanni sun nuna cewar ana matukar bukatar tsabtataccen ruwan sha da magunguna ga mutanen da suka tsira da ransu.

Wani likita a babban asibitin yankin ya shaidawa BBC cewar suna kokarin shawo kan matsalar.

Galibin gidajen kauyen an gina su da laka ne abinda ya janyo lamarin ya kara muni.

Karin bayani