Mutane 24 ne suka mutu a birnin Khartoum

Sudan
Image caption An daina aiki a makarantu da gidajen jaridu

Akalla mutane 24 ne suka mutu a birnin Khartoum na Sudan a rana ta uku ta zanga zangar da ake gudanarwa sakamakon zaftare kudaden tallafin man fetur.

Daraktan asibitin Omdurman ya fadawa sashen Larabci na BBC cewa harbe mutanen aka yi.

Ya kara da cewa ana yiwa wasu mutane kimanin 80 magani bayan raunin harsashin da suka samu.

Tunda farko dai 'yan sanda sun harba hayaki mai sa hawaye ga masu zanga zangar wadanda suke jifa da duwatsu, a yayinda zanga zangar ta barke a wasu sassan babban birnin Kasar.

Shaidu sun ce masu zanga zangar sun cinnawa wani ginin jami'a wuta da kuma gidajen saida mai da dama.

Haka kuma sun tare babban titin daya dangana zuwa filin jirgin saman babban birnin.

Karin bayani