Rarrabuwa tsakanin 'yan tawayen Syria

Image caption Dan tawaye a Syria

Kungiyoyin 'yan tawaye 11 wadanda galibinsu masu kishin Islama ne a Syria sun yi bara'a ga hadaddiyar kungiyar 'yan adawa da kuma gwamnatin riko wacce ke kasashen waje.

A wata sanarwar hadin gwiwa, sun ce 'yan tawayen dake zaune a kasashen waje wadanda ba shigo cikin Syria sun hade da 'yan tawaye ba, ba sa wakiltarsu.

Kungiyoyin da suka sanya hannu a sanarwar sun hada da wakilan Free Syrian Army da kuma Al-Nusra Front wacce keda alaka da Alka'ida.

Wakilin BBC yace sanarwar wata manuniya ce a kan cewar al-Nusra na da karfi sosai, abinda ke jefa fargaba ga kasashen yammacin duniya wace goyon bayan 'yan adawa.

Kungiyoyin kuma sun yi kira a tabbatar da tsarin shari'ar musulunci a Syria.

Karin bayani