Dan wani babban soja a China zai sha dauri

Image caption Li Tianyi, zai shafe shekaru 10 a kurkuku

Wata kotu a Beijing ta yanke hukuncin daurin shekaru goma a kan wani matashi bisa laifin hannu wajen yin taron dangi su aikata fyade.

Matashin mai shekaru sha bakwai dan wani fitacen janar din sojan kasar ta China.

Wannan shari'a ta Li Tianyi ta janyo cece kuce tsakanin jama'a a kasar ta China kan irin yadda 'ya'yan manyan kasar ke cin karensu ba- babbaka.

Shi dai Li Tianyi na daya daga cikin mutane biyar ne da ake zargi da cin zarafi, da kuma haduwa su aikata fyade kan wata mata a wani otel a birnin Beijing.

Karin bayani