Za a kara kudin ruwa da wuta a Ghana

Image caption Shugaban Ghana, John Dramani Mahama

Al'ummar kasar Ghana sun nuna takaicinsu game da karin kudin wutan lantarki da na ruwan fanfo da gwamnatin kasar ke shirin yi.

A yammacin ranar Laraba ne, gwamnatin Ghana ta sanar da karin kudin wuta da kashi 78 cikin 100, da kuma karin kudin ruwan fanfo da kashi 52 cikin 100.

Sanarwar da gwamnati ta fitar, ta ce sabon karin kudin zai soma aiki ne daga ranar Talata mai zuwa.

A shekara ta 2010 ma sai da gwamnatin kasar ta kara kudin ruwa da wutan lantarki.

Karin na zuwa ne a lokacin da wasu talakawan kasar ke kokawa game da kuncin rayuwa.

Karin bayani