An kashe mutane 12 a Kashmir

Image caption Ana zaman doya da manja tsakanin Pakistan da India kan yankin Kashmir

An yi barin wuta tsakanin mayaka da jami'an tsaro a yankin Kashmir da India ke iko dashi, inda mutane 12 suka mutu.

Jami'ai sun ce mayaka dauke da manyan makamai cikin kayan sarki sun bude wuta a wani caji ofis dake kan iyaka da kasar Pakistan.

Jami'an tsaron India na ci gaba bata kashi da maharan a wani sansanin soji.

Piraministan India Manmohan Singh ya bayyana harin a matsayin abinda zai yi kafar angulu wajen tabbatar da zaman lafiya.

A cikin wannan makon ake saran Piraministan India dana Pakistan za su tattaunawa a wajen taron Majalisar Dinkin Duniya.

Karin bayani