Iran na son yarjejeniyar nukiliya a wata uku

Cibiyar nukiliyar Iran
Image caption Cibiyar nukiliyar Iran

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya ce ya na fatan cimma yarjejeniya game da makamashin nukiliya da kasashen masu fada aji na duniya cikin watanni uku zuwa shida.

Mr. Rouhani ya shaidawa jaridar Washington Post cewa a shirye Iran take ta bada dukkan bayanana da kasashen Yamma ke bukata domin gamsar da su cewa ba ta da niyyar kera makamin nukiliya.

Ya kuma ce ya samu cikakken goyon bayan jagoran juyin juya halin Iran Ayatollah Khamenei game da tattaunawar.

A ranar Alhamis ne dai Iran za ta tattauna da Burtaniya, da Faransa, da Jamus, da Rasha, da China, da Amurka game da batun na nukiliya.

Tuni dai Ministan hulda da kasashen waje na Iran Mohammad Javad Zarif ya gana da takwaransa na Faransa Laurent Fabius game da batun nukiliyar.

Yace; "mun gana game da batun tattaunawa akan shirinmu na nukiliya; da zaman da za'a yi gobe tsakanin ministocin kasashen wajen Iran da sauran kasashe shida. Iran dai a shirya ta ke ta tattauna wannan lamari. muna kuma fatan su ma daya bangaren sun kimtsa."

Karin bayani