An bude taro kan ingancin zabe a Najeriya

Kidaya takardar kada kuri'a lokacin zabe a Najeriya
Image caption Wani jami'i na kidaya takardar kada kuri'a lokacin zabe a Najeriya

An bude wani taron kasa da kasa kan musayar bayanai game da yadda za a shirya zabe na gari a shekarar 2015 a Najeriya.

Ana so ne jami'an zabe da 'yan jaridar kasar su koyi irin dubarun da wasu kasashe ke amfani da su, wajen shirya sahihin zabe.

Taron ya samu halartar 'yan jarida daga kasashen Ghana da kuma Congo, inda suka yi musayar bayanai game da yadda aka yi zabuka masu inganci da kuma irin kalubalen da suka fuskanta.

Mutane da dama a kasar na fatan ganin an yi ingantacce zabe ta yadda al'umma za su gamsu a cikin kasar baki daya.