Najeriya ta yi martani kan bidiyon Shekau

Wani soja a cikin mota mai sulke
Image caption A watan jiya ne rundunar tsaro ta JTF ta ce watakila Sheakau ya mutu ta raunin harbin bindiga

Mai baiwa shugaban Najeriya shawara kan hulda da jama'a, Dr. Doyin Okupe ya maida martani a kan faifan bidiyon da ke nuna shugaban kungiyar da aka fi sani da Boko Haram Abubakar Shekau na raye.

Jami'in dai ya ce da ma sojoji ba su ce tabbas ya mutu ba, abin da suka ce shi ne akwai yiwuwar ya mutu a wata arangama da suka yi da 'yan kungiyar.

A hira da BBC Mr. Okupe ya ce babu wani batun jin kunya daga bagaren hukumomi, tun da an sha fadar mutuwar shugabannin AlQaida a kafafen yada labaran kasashen waje, amma daga bisani su fito a bidiyo su musanta.

Sai dai ya amince sake bayyanar Shekau wani babban kalubale ne, ko da yake a cewarsa dakarun kasar na cin galaba a yaki da suke yi da 'yayan kungiyar.