An tabbatar wa Taylor daurin shekaru 50

Tsohon shugaban kasar Liberia, Charles Taylor
Image caption Mai shigar da kara ya nemi a kara yawan shekarun daure Mr. Taylor

Kotu ta musamman dake zamanta a Hague, da ke da goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da daurin shekaru 50 a kan tsohon shugaban kasar Liberia Charles Taylor.

Alkalin kotun ya ce an yi adalci a hukuncin da aka yanke masa game da samunsa da laifin taimaka wa 'yan tawaye a lokacin yakin basasar Saliyo.

Kotun ta yi watsi da karar da Mr. Taylor ya daukaka a gabanta, a zaman da tayi a ranar Alhamis.

Ko da yake lauyansa ya nemi a soke hukuncin tare da wanke Charles Taylor, saboda kuskuren da yace an samu a lokacin shari'ar baya.

Mr. Taylor ne tsoshon shugaban kasa na farko da kotun ta samu da laifi, tun bayan shari'a Nurenberg da ya shafi Nazis.