'Ana soma dasawa tsakanin Iran da Amurka'

Image caption Shugaba Hassan Rouhani

Shugaban Kasar Iran Hassan Rouhani, ya ce an dan samu kyautatuwar al'amurra tsakanin Iran da da Amurka, in aka kwatanta da a baya.

A lokacin wani taron manema labaru, a karshen ziyarar da ya kai ta kwanaki hudu, a Majalisar Dinkin Duniya dake New York, shugaba Rouhani ya ce tattaunawa kan nukiliyar Iran tsakanin ministan harkokin wajensa da sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry, sun yi armashi, suna kuma da karfafa gwiwa.

Shugaba Rouhani ya ce bai gana da shugaba Obama ba, saboda babu isasshen lokaci na shiryawa ganawar.

Shekaru talatin da biyar kenan ana yi ma juna kalon hadarin-kaji tsakanin Iran da Amurka, amma Rouhani ya ce abu ne da zai kasance mai sarkakiya.

Karin bayani