An kashe jami'an tsaro a Saminaka

Wasu sojojin Najeriya
Image caption Wasu sojojin Najeriya

Rahotanni daga jihar Kaduna na cewa wani soja da 'yan sanda biyu sun rasa rayukansu, a wani harin da aka kai a garin Saminaka dake kudancin jihar.

Wasu mutane da ba a san ko su wanene ba dauke da bindigogi suka kai harin, a kan wasu bankuna biyu da ke garin a ranar Alhamis da daddare.

Mazauna garin sun ce an shafe sa'oi ana dauki-ba-dadi tsakanin maharan da jam'an tsaro.

Ana dai cigaba da samun hare-haren a garuruwan dake wajen manyan birane a jihohin arewacin Najeriya, duk da ikirarin hukumomi na cewa sha'anin tsaro ya inganta a yankin.