Mata za su bijirewa haramcin tuki a Saudiyya

Wata mata da ta taka dokar haramta tuki a Saudiyya
Image caption Ba a hukumance bane aka haramta wa mata tuka mota a Saudiyya

Mata fiye da dubu 11 ne suka rattaba hannu domin nuna goyon bayansu ga wani kamfe, na baiwa mata 'yancin tuka mota a kasar Saudi Arabia.

Masu kamfe din sun tsayar da ranar 26 ga watan Oktoba, a matsayin ranar da mata za su fito kwansu da kwarkwatarsu su tuka mota a kasar.

Kamfe din da ake yi ta shafin intanet ya nemi hukumomin Saudiyya da su bayyana kwakkwarar hujja a karkashin shari'a, idan har kasar ta cigaba da hana mata tuki.

Yunkurin bijirewa haramcin da wasu mata masu fafutuka suka yi a shekarun baya a kasar, ya janyo an kama su ko kuma korarsu daga aiki.