Rasha da Amurka sun daidaita kan Syria

Image caption Wannan yarjejeniyar tsakanin Rasha da Amurka ta kawo karshen makonnin na kace-nace da kuma shekaru biyu da rabi na ja-in-ja kan batun Syria a kwamitin tsaron.

Kasashen Amurka da Rasha sun cimma matsaya kan wani daftarin kudurin Majalisar Dinkin Duniya, domin raba Syria da makamai masu guba.

An zagaya da daftarin ga kasashen masu wakilci a kwamitin tsaro na Majalisar, a ranar Alhamis da dare in da suka rattaba hannu.

Jami'an diplomasiyya a birnin New York sun ce za a iya amincewa da shi nan da yammacin ranar Jumu'a.

Yarjejeniyar za ta bukaci Syria ta mika makamai masu gubarta, amma ba tare da yi mata barazanar yin amfani da karfin soji idan ta ki ba, amma duk lokacin taki ba da hadin kai za a mika batun ga Kwamitin tsaron domin kara tattaunawa.

Wannan dai shi ne karon farko da Kwamitin tsaro na Majalisar ya samu shawo kan rarrabuwar kawunan da ake da shi kan Syria.

Karin bayani