Gwamnatin Zamfara na duba koken zawarawa

Gwamnan jihar Zamfara, Alhaji AbdulAziz Yari
Image caption Zamfara ce jihar farko da ta fara aiwatar da shari'ar musulunci a Najeriya

Gwamnatin Jihar Zamfara a Najeriya ta ce tana duba koken da wasu mata kimanin dubu takwas suka yi na neman a taimaka musu su samu mazajen aure.

Matan dai sun yi wani maci ne a Gusau babban birnin Jihar, zuwa shalkwatar hukumar Hizbah ta Jihar a ranar Alhamis.

Kuma sun nemi gwamnati da ta dauki salo irin na gwamnatin Jihar Kano, domin ganin sun samu mazajen aure.

Shugaban hadaddiyar kungiyar zawarawa ta Jihar Zamfarar, Sa'idu Alhaji Goshi ya ce kungiyar tana da rijistar zawarawa fiye da dubu 8, wadanda wadansunsu sun shafe fiye da shekaru 16 ba aure.