Mata 8,000 sun yi zanga-zanga a Zamfara

Image caption Gwamna Abdulaziz Yari

A jihar Zamfara dake arewacin Najeriya wasu mata kusan dubu takwas ne suka yi zanga-zanga don neman gwamnatin jihar ta tallafa musu ta auraddasu.

Matan wadanda suka yi zanga-zangar sun bukaci gwamnatin jihar ta duba irin tsarin da ake bi a jihar Kano don aurar da mata zaurawa da kuma 'yan mata.

Korafin matan dai shine cewar suna fuskantar matsalalolin rayuwa, kuma idan aka samar musu mazan aure, zasu samu saukin rayuwa.

Kwamshinan harkokin addinin Musulunci a jihar Zamfara, Farfesa Abdullahi Muhammed Shinkafi a hirarsa da BBC ya ce gwamnati za ta duba bukatar matan.

Karin bayani