Takun sakar 'yan siyasa a kasar Girka

Nikos Michaloliakos
Image caption Shugaban jam'iyyar adawa ta Golden Dawn a kasar Girka

'Yan sandan kasar Girka sun kama shugaban jam'iyyar nan ta masu tsananin ra'ayin rikau ta Golden Dawn, Nikos Michaloliakos, kan zargin kasancewa dan wata kungiya ta masu aikata miyagun laifukka.

Akwai wasu karin mutane sha shidan da aka kama ,wadanda su ma suna da alaka da jam'iyyar ta masu ra'ayin 'yan Nazi, ciki har da wasu 'yan majalisar dokoki uku.

An yi kamen ne bayan kasan da ake zargin wani dan jam'iyar ta Golden Dwan ya yi ma wani mai fafutuka dake da ra'ayin sauyi, kuma mawakin salon kida na Rap, kwanaki goma da suka wuce.

Kimanin magoya bayan jam'iyyar ta Golden Dawn dari biyu ne suka taru a kofar ofishin 'yan sandan da ake yi wa mutanen tambayoyi.

Ana danganta jam'iyyar mai wakilai sha takwas a majalisa da hare hare a kan baki 'yan kasashen waje, da nuna wariyar launin fata.