Yau ake zabe a kasar Guinea

Image caption Kungiyoyin 'yan adawa sun zargi jam'iyyar Shugaba Alpha Conde da kokarin tafka magudi.

Al'ummar kasar Guinea na kada kuri'a a yau Assabar, domin zaben 'yan majalisar dokoki wanda aka dauki tsawon lokaci ana shiryawa.

Wannan dai wani muhimmin mataki ne ga shirin kasar da ke yammacin Afrika na komawa kan tsarin dimokradiyya bayan juyin mulkin da aka yi a shekara ta 2008.

Tashe-tashen hankula ne suka wargaza shirye-shiryen zaben da kuma zaman zullumin da yayi kamari saboda bambance-bancen kabila da addini.

A da dai an shirya gudanar da zabukan ne cikin watanni 6 Shugaba Alpha Conde ya karbi mulki a shekara ta dubu 2010.

Karin bayani