Iran da Amurka na san kulla zumunta

Dinbim jama'a ne suka yi dafifi domin tarbar shugaban kasar Iran, Hassan Rouhani a filin jiragen sama na Mehrabad dake Tehran, lokacin da ya koma gida daga New York, kwana guda bayan yayi wata tattaunawar minti sha biyar mai cike da tarihi, da shugaba Obama ta waya.

Wasu gungun jama'ar sun rika nuna gamsuwa ga matakan diplomasiyyar da shugaba Rouhani ya dauka , yayinda wasu masu zanga zanga sama da su dari daya, suka rika Allah wadai suna jifansa da takalma.

Tattaunawar ta waya tsakanin shugaba Rouhani da shugaba Obama ita ce ta farko tsakanin shugabannin kasashen biyu cikin sama da shekaru talatin.