Shugaban Italiya na barazanar yin Murabus

Image caption Fara ministan Italiya Enrico Letta

Fara Ministan Italiya Enrico Letta ya yi kashedin yin murabus muddin gwamnatinsa ta gaza samun goyon baya a wata kuri'a da za a yi a majalisar dokoki cikin wasu 'yan kwanaki masu zuwa.

Wannan barazanar dai wadda ta kara dagula al'amurra a fagen siyasar kasar ta Italy wanda ke cikin rikici; ta zo ne bayan taron majalisar ministoci da aka kai talatainin dare ana yi wanda ya gaza cimma matsaya a kan wani muhimmin batu da ya shafi kasafin kudin kasar.

Gwamnatin ta Mr Letta dai wani bahagon gamin-gambiza ne tsakanin jam'iyyarsa mai ra'ayin kawo sauyi da ta masu ra'ayin rikau a karkashin jagorancin tsohon fara minista Silvio Berlusconi.

Shi ma Mr. Berlusconi yana fuskantar yiwuwar kora daga majalisar dattawan kasar sakamakon samunsa da laifin almundahana da kudaden haraji.

Karin bayani