Hukumomin Nijer na kokarin cimma muradun karni

Shugaba Issofou na Nijer
Image caption Nijer na kokarin cimma muradun karni na samad da ruwa ga jama'a

Yayinda shekara ta 2015 ke karatowa wa'adin da Majalisar Dinkin Duniya ta gindaya na cimma muradun karni wadanda suka hada da batun samar da tsaftaccen ruwan sha da muhalli ga jamaa, kasashe da kungiyoyi masu zaman kansu na hada karfi da karfe domin hakar su ta cimma ruwa a wannan fanni.

A yanzu haka wata kungiya mai zaman kanta a Faransa da ake kira PS-Eau ( Pe- S-O) da Hukumar tsaftace muhalli ta birnin Paris, SIAAP (Siyap) sun yi wani babban taro a birnin na Paris a jiya tare da wakilan ma'aikatar samar da ruwan sha ta Jumhuriyar Nijar da kuma wasu magaddan gari na Nijar don ganin yadda za a taimaka wajen kyautata muhallin jamaa a kasar ta Nijar.