An amince da kudurin lalata makaman Syria

Image caption Mr Moon ya ce akwai bukatar yin abin da ya fi wannan domin kawo karshen fadan da ya halaka mutane sama ga dubu dari.

Wakilan Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin duniya sun amince ga baki dayansu da a lalata makaman gubar Syria lokacin da suka jefa kuri'a kan batun ranar jumu'a da dare.

Kuria'r wadda ta zo bayan an kwashe makonni biyu na tattaunawa mai zurfi, ta zamo wani babban cigaba bayan rarrabuwar kawunan da ta dabaibaye kwamitin tun bayan da rikicin ya soma.

''Wannan kudurin na tarihi ya zame labari mai sanya fata ta gari na farko kan Syria a cikin lokaci mai tsawo'' inji Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniyar Ban ki Moon a jawabin da yayi bayan jefa kuri'ar.

Kudurin dai ya yi kiran ladabtarwa idan Syrian ta ki bin tanade-tanadensa, sai dai ita ma ladabtarwar za ta dogara ne kan sakamakon wata kuri'ar da kwamitin zai kada idan har Syriar ta yi hakan.

A baya dai kasashen Rasha da China sun yi ta hawan kujerar-naki ga kudurorin da kasashen yamma ke gabatarwa da ke neman a matsawa shugaba Assad lamba.

Karin bayani