Ana tattara sakamakon zabe a Guinea

Image caption Masu zabe miliyan biyar ne suka yi rijistar jefa kuri'a a zaben.

An kammala gudanar da zaben Majalisar dokoki a Guinea Conakry a karon farko cikin fiye da shekaru goma.

Alamun farko sun nuna cewar mutane da dama sun fita domin kada kuri'unsu, duk da yake dai an ba da rahoton fuskantar wasu 'yan matsaloli.

A ranar talata ne ake sa ran samun sakamakon farko na zaben.

An samu tashe-tashen hankula a lokacin yakin neman zaben, sai dai kuma ba a fuskanci wasu manyan matsaloli ba a lokacin gudanar da shi.

Tun cikin watannin farko na mulkin rikon-kwarya na Shugaba Alpha Conde a shekara ta 2010 ne aka so gudanar da zaben- bayan wani juyin mulkin soji, amma aka jinkirta shi.