"Ana farautar maharan Gujba". Inji JTF

Dakarun JTF
Image caption Dakarun JTF

Rundunar sojan Nijeriya ta ce wasu da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari kan wasu gidajen kwanan dalibai a wata makarantar koyon aikin noma dake jihar Yobe, yayinda daliban ke barci.

Wani dan siyasa na yankin ya shaida wa BBC cewa an kashe mutane hamsin; ya ce an cika motocin daukar kaya biyu da gawarwaki zuwa asibitin Damaturu, hedkwatar jihar.

Majiyar sojan ta ce wasu 'yan bindiga ne suka shiga dakunan kwanan, lokacin da dare ya tsala, suka rika barin wuta a kan daliban.

An kuma ce sun cinna wuta a kan azuzuwan makarantar dake karamar hukumar Gujba.

Maharan sun je makarantar ne a cikin mota kirar Hilux da babura.

Wannan dai ba shi ne karan farko da ake kai hari makarantar kwana ba a wannan jahar ta Yobe ba.