Kenya ta musanta gargadi daga Al-Sahaab

Uhuru Kenyatta
Image caption Shugaban kasar Kenya

Gwamnatin Kenya ta yi watsi da rahotannin dake cewa, ana jin sun yi biris da wani gargadi na kungiyar Al-Shabaab game da yuwuwar kai farmaki.

Wasu jaridun kasar na cewa hukumar leken asirin kasar ta ce shekara guda da ya wuce , wasu da ake zargin mayakan sa kai ne na shirya kai hare hare a wasu wurare ciki har da rukunin shaguna na Westgate.

Akwai rahotannin wani sabon gargadin game da wasu hare haren a wannan wata.

A gobe ne ake sa ran wasu jami'an tsaro zasu bayyana a gaban wani kwamitin majalisar dokoki domin amsa tambayoyi kan zargin gazawar jami'an leken asirin.

Mutane akalla sittin da bakwai ne aka tabbatar da sun mutu a hareharen na Westgate.