Fada ya barke a Mali

sojan Mali a garin Kidal
Image caption Fadan ya kawo cikas ga shirin dakatar da bude wuta da sabuwar gwamnatin ta sa a gaba

Fada ya barke a garin Kidal na arewacin Mali inda ake zargin mayakan Abzinawa da kai hari kan sojin gwamnati.

An ruwaito gwamnan lardin, Adama Kamissoko yana cewa ana ta musayar wuta a garin na Kidal.

Kwanaki uku da suka wuce 'yan awaren sun ba da sanarwar za su kawo karshen tsagaita wutar da suka yi da sabon shugaban kasar Malin Ibrahim Boubakar Keita.

wanda ya sha alwashin ba da fifiko kan harkokin tsaro.

Ranar Asabar an kai wani harin kunar-bakin-wake a mota a kofar wani sansanin soja a birnin Timbuktu.

Harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu.