Nijar ta shirya mahawara kan safarar mutane

shugaban nijar mahamadou issoufou
Image caption Njiar na son hana amfani da kasarta wajen safarar mutane

Ma'aikatar shari'a ta jamhuriyar Nijar ta shirya wata mahawara kan yaki da safarar mutane.

Taron ya hada dukkanin masu ruwa da tsaki kan yaki da matsalar ta safarar bil'adama kan yadda za a hana amfani da kasar wajen wucewar masu safarar.

Bincike dai ya nuna Nijar a matsayin wani wurin yada zango ga masu shirin shiga kasashen larabawa ko Turai.

Wasu daga cikin mutanen da ake safarar tasu ana sanya su ayyukan ashsha a kasashen da ake kai su.