Za mu je Kotu kan kisan Apo - Dr. Funtua

Image caption Su dai mutanen sun musanta cewa 'yan kungiyar Boko Haram ne su.

Wasu 'yan majalisar dokokin Najeriya daga yankin da wasu daga cikin mutane 9 da jami'an tsaron kasar suka kashe a Abuja bisa zargin cewa 'yan kungiyar Boko Haram ne suka fito sun sha alwashin zuwa kotu domin bi masu hakkinsu.

'' Bai yiwuwa a kasar da ake da doka da ka'ida a ce haka kawai an far ma wasu mutane an hahharbe su bisa zargi'' inji Dr Mansur Abdulkadir Funtua, Dan majalisar wakilai daga mazabar Funtua/Dandume a cikin wata hira da BBC.

Ya ce shi da wasu takwarorinsa 7 da lamarin ya shafi mazabunsu sun hadu sun cimma matsaya daukar matakin shara'a kan jami'an tsaron Najeriyar.

Yanzu haka dai ana ci gaba da jiran sakamakon bincike kan kisan na ranar 20 ga watan Satumba a Unguwar Apo dake birnin na Abuja; inda jami'an tsaron suka kashe mutane 9 'yan ci-rani suka kuma raunata karin wasu, lokacin da suka kai samame a wani kangon gida da suke kwana da tsakar dare.

Karin bayani