Ban ki moon ya gana da yan adawar Syria

Ahmed al Jarba Shugaban kungiyoyin adawar Syria
Image caption Shugaban Kungiyar gamayyar kungiyoyin adawa na Syria ya gana da Sakataren Majalisar Dinkin Duniya

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Banki Moon ya gana da Shugaban gamayyar kungiyoyin 'yan adawa na Syria Ahmed al-Jarba a birnin New York a daidai lokacinda ake kokarin lalubo hanyoyi na diplomasiyya na kawo karshen yakin da ake yi a kasar ta Syria.

Bayan ganawar ta su, Mr Ban ya fada a wata sanarwa cewar Mr Al Jarba a shirye yake ya aike da wakilai zuwa taron zaman lafiyar da aka shirya a tsakiyar watan Nuwamba wanda aka yi ma lakani da Geneva 2.

Sakatare Janar din ya yi kira ga gamayyar kungiyoyin 'yan adawar na Syria su gama kai su tsaida wakilai ga taron zaman lafiyar.

Karin bayani