An kashe dalibai sama da 40 a Yobe

mayakan boko haram
Image caption Maharan sun dauki sama da sa'a daya suna kai harin a makarantar

Wasu mahara da ba a san ko su wane ne ba sun kai hari kwalejin koyon aikin gona ta Gujuba a jihar Yobe a Najeriya suka kashe dalibai 42.

Maharan wadanda aka ce suna sanye da kayan soji sun kuma jikkata wasu daliban guda biyar.

Rundunar tsaro ta hadin guiwa ta JTF ta Yobe ta ce tana gudanar da bincike amma ta ce tana ganin maharan 'yan kungiyar Boko Haram ne.

Mutanen sun kai harin ne da misalin karfe daya na daren ranar Asabar din nan da ta gabata.

An kai jami'an tsaro makarantar wadda ke da nisan kilomita 40 daga Damaturu, yayin da dalibai ke ci gaba da barin kwalejin.