Faraminista Abbot na ziyara a Jakarta

Image caption Batutuwan da suka shafi iyaka sun jima suna ci ma kasashen biyu tuwo a kwarya.

Sabon Faraministan Australia Tony Abbott yana ziyara a Indonesia a daidai lokacinda rayukka suka baci tsakanin kasashen biyu dangane da manufarsa game da masu neman mafaka.

A ziyarsa ta farko zuwa wata kasa tun bayan zabensa a farkon wannan watan, Mr Abbott yana son karfafa huldar dangantakar kasuwani ne dake tsakanin kasashen biyu.

Mr. Abbot dai ya isa birnin Jakarta ne kwanakki uku bayan wani jirgin ruwa da ke dauke da masu neman mafaka da ya nufi Australiya ya nutse a tekun Indonesia , inda ya kashe mutane 29 wasu kuma suka bata.

Dubban mutane ne ke hawan jiragen kamun kifi marasa kwari a kowace shekara domin tafiyar mai hadari ta tsawo kilomita 500 aka doron teku.

Da Mr. Abbot ya karbi mulki makonni biyu da suka wuce ya yi alkawalin dakatar da zuwan jirage ruwan masu jigilar masu neman mafaka zuwa kasarsa.

Amma sai Indonesiya ta nuna damuwa ga shirin na Mr. Abbot wanda ya hada da baiwa sojan ruwa Australiya damar tarewa da kuma mai da jiragen kamun kifi na Indonesiya da ke makare da masu neman mafaka inda suka fito.

Karin bayani