Yau ake zaben 'yan majalisa a Kamaru

Image caption Kowane bangare dai na da fatan yin galaba

A yau Litinin ne ake gudanar da zabukan 'yan majalisar dokoki da na kananan hukumomi a Jamhuriyar Kamaru da ke tsakiyar Afrika.

Wadannan zabukan biyu da suka hada kan jam'iyyu da dama za su gudana ne a lokaci guda a duk fadin kasar.

Hukumar zaben kasar dai ta ce ta kammala dukkan shirye-shiyre na ganin an samu nasarar gudanar da zabukan.

''Kujerun majalisar dokokin 180 ne dai jam'iyyun suke takara a mataki na farko na tagwayen zabukan da za a fara a yau; kana daga bisani za a jefa kuria domin zaben kansilolin sama ga dubu goma.'' A cewar wakilin BBC a birnin Yaounde.

Karin bayani