Zaben 'yan majalisa da kansuloli a Kamaru

Image caption Shugaba Paul Biya na Kamaru

A Kamaru masu kada kuri'a fiye da miliyan biyar ne ake sa ran zasu zabi 'yan majalisar dokoki dari da tamanin da kuma kansuloli dubu goma.

A zabukan baya dai 'yan adawa sun sha zargin gwamnatin Paul Biya da rashin tsaida takamaiman lokacin zaben 'yan majalisa domin tabbatar da rinjiyen jam'iyyar RDPC mai mulki.

Sai dai jam'iyyar ta RDPC na musanta wannan zargi.

Wakilinmu Muhamman Babalala wanda ke sa ido a kan zaben birnin Younde ya ce bisa dukkan alamu jam'iyyar dake mulki ta tsora da fitowar jama'a a runfunan zabe.

Karin bayani