'Za a sauya sallon yaki da Boko Haram'

Image caption A yanzu dai mayakan kungiyar kan yi shiga irin ta sojojin Najeriya idan za su kai hare-hare.

Shugaban Najeriya Dr. Goodluck Jonathan ya ce gwamnati na tsara sabbin dabarun yaki da kungiyar jama'atu ahlisunnah lidda'awati wal jihad wadda aka fi sani da Boko Haram.

Shugaban ya yi wannan bayanin ne a wata tattaunawar da ya yi da 'yan jarida da aka nuna kai-tsaye ta wasu gidajen tallabijin na kasar, inda yace sabon salon da 'yan kungiyar suka fito da shi wajen kai hare-hare na bukatar sabbin dabaru.

Ya ce bai ji dadin yadda sha'anin tsaro ya tabarbare a jahohin Borno da Yobe ba; bayan rikicin yayi kamar ya lafa a yankin bayan saka dokar-ta-baci. '' Sun koma kai hari kan wurare masu saukin kai wa hari da nufin tozarta gwamnati.'' Inji shi.

Kalaman nasa sun zo ne kasa ga kwana daya bayan wasu mayakan da ake ji 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari kan wata makaranta a jahar Yobe inda suka kashe dalibai sama ga 40.

Karin bayani