Westgate: 'Yan majalisa sun soma bincike

Image caption Mutane suna jimamin rasuwar 'yan uwansu

'Yan majalisar dokokin Kenya sun soma gudanar da bincike, a kan harin da aka kaiwa babbar cibiyar kasuwancin Nairobi a makon jiya.

Mambobin kwamitin tsaro sun ziyarci cibiyar kasuwancin ta Westgate, domin gane wa idanunsu irin ta'adin da aka yi.

A 'yan kwanaki masu zuwa ana sa ran 'yan majalisar, zasu yi wa manyan jami'an tsaron kasar tambayoyi, kan zarge-zargen cewa, an sami kasawa ta fuskar leken asiri.

Akalla mutane sittin da bakwai ne suka hallaka.

Kungiyar agajin Red Cross ta Kenyar ta ce, mutane talatin da tara ne har yanzu ba a ji duriyarsu ba.

Karin bayani