Tattalin arzikin duniya zai shiga uku -- Inji Obama

Barack Obama
Image caption Barack Obama, Shugaban Amurka

Shugaba Obama, ya yi gargadin cewa muddin majalisar dokokin Amurka ta ki kara yawan adadin bashin da gwamnati za ta iya karba to kuwa tattalin arzikin duniya zai fada cikin rashin tabbas kuma Amurka za ta kasance cikin bashi na din-din-din.

Ya ce idan hakan kuma ya faru to kasar za ta koma cikin matsalar tabarbarewar tattalin arziki, kuma zai zama karon farko da Amurka za ta gaza aiwatar da bukatunta ta fuskar kudade.

Nan da kwanaki tara masu zuwa ne wa'adin kara yawan bashin da Amurka za ta iya ci zai cika a majalisar dokokin.

Mr Obama ya ce idan har haka ba ta faru ba, a karon farko kenan Amurka za ta gaza wajen biyan bashin dake kanta a cikin shekaru fiye da 200.

Tun farko dai babban masanin tattalin arziki na hukumar bayar da lamuni ta duniya -IMF ya ce kasa biyan bashin zai iya haddasa abinda ya kira manyan matsaloli.

Karin bayani