China za ta gina babban asibiti a Nijar

Image caption Shugaba Muhammadou Issoufou

A jamhuriyar Nijar, Shugaban kasar Alhaji Mahamadou Isoufou ya jagoranci bikin kaddamar da soma aikin gina wani babban asibiti da kasar China ta dauki nauyin gudanarwa.

Asibitin dai zai kasance mai gadaje dari biyar, kuma zai kasance asibiti mafi girma da kasar China ta gina a nahiyar Afirka.

Rahotanni sun nuna cewar za a kashe kusan CFA biliyan 27 wajen gina katafaren asibiti.

China dai tana dasawa da Nijar, kuma ta zuba jari a fannin man fetur da sauran ma'adinai na kasar.

Karin bayani