Cece-kuce kan taron kasa a Najeriya

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan
Image caption Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan

Jama'a a Najeriya na ta maida martani ga sanarwar da shugaba Goodluck Jonathan ya yi, na kafa wani kwamiti wanda zai bada shawara a kan yadda za a shirya wani babban taro na kasa.

A jawabinsa ga al'ummar kasar domin bikin shekaru 53 da samun 'yancin kan Najeriya daga turawan mulkin mallaka, Shugaban ya ce kwamitin ne zai fito da tsare-tsare da kuma fasalin yadda taron zai kasance.

Har ila yau Shugaban ya kuma tabo batun halin tabarbarewar sha'anin tsaron da ake fama da shi a kasar, musamman a wasu jahohin arewacin kasar, inda ya nanata cewa gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba, wajen tabbatar da tsaron lafiyar jama'a.

An dade ana cece-kuce tsakanin al'ummar kasar a kan batun yin taron hada kan kasa, wanda masu sharhi ke ganin shi ne mafita domin sanin makomar kasar.

Amma wasu na ganin taron ba zai yi tasiri ba, saboda shugaba Goodluck ne da kansa ya kafa kwamitin mai bada shawara.

Karin bayani