Matsalar yunwa ta karu a duniya

Image caption Mutane da dama Afrika na fama da yunwa

Wani rahoton hukumar abinci ta majalisar dinkin duniya yace, mutum daya cikin takwas a duniya na fama da matsalar yunwa.

Rahoton wanda yayi waiwaye a kan matsalar cikin shekaru biyun da suka gabata ya ce, mutane fiye da miliyan 800 suna fama da karancin abinci mai gina jiki.

Duk da cewa alkaluman da wannan rahoto ya fitar na nuna raguwar matsalar idan aka kwatanta da bara, amma rahoton yace, ba'a samu cigaban a zo a gani ba a kasashen kudu da hamadar Sahara na Afurka da kuma yammacin nahiyar Asiya.

Rahotan ya yi gargadin cewar akwai matukar yuwa ba za a cimma muradun karni daga nan zuwa 2015 ba a kan batun rage yawan mutanen dake fama da yunwa a duniya.