Hare-hare a kauyukan jahar Zamfara

Gwamnan jahar Zamfara, Abdulaziz Yari Abubakar
Image caption Gwamnan jahar Zamfara, Abdulaziz Yari Abubakar

Wasu 'yan fashi da makami sun kai hari a wasu kauyuka a karamar hukumar Bukkuyum da ke jihar Zamfara.

An sami asarar rayuka da kuma dimbin dukiya.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC cewa, 'yan fashin sun hallaka mutane 5 kuma sun kora shanu fiye da dari da sauran kananan dabbobi masu yawa.

Ya ce mutanen gari sun samu sun kashe daya daga cikin maharan.

Gwamnan jahar Zamfarar, Dokta Abdulaziz Yari Abubakar, ya ziyarci karamar hukumar ta Bukkuyum, domin gane wa idanunsa irin ta'asar da aka yi.

Mashawarcin musamman ga gwamnan kan kafofin yada labarai da sadarwa, Alhaji Sani Abdullahi Tsafe, ya gaya wa BBC cewa rahotannin farko sun nuna cewa mutane 3 ne su ka rasu a hare haren.

Gwamnan ya bada umurnin a kara tsaurara matakan tsaro domin gano 'yan fashi da makamin.

Mazauna kauyukan da suka hada da mata da kananan yara sun yi gudun hijira domin gudun ramuwar gayya daga 'yan fashin.

Duk da matakan da hukumomin yankin suke cewa suna dauka don magance matsalar fashi da makami da aka sha fuskanta, har yanzu ba a gano bakin zaren lamarin ba.