ICC ta bada sammacin kama dan jarida

Walter Baraza
Image caption Walter Baraza

Kotun hukunta manyan laifukan yaki ta duniya, ICC ta bada sammacin kama wani dan jarida a Kenya, bisa zargin yin katsalandan a shari'ar mataimakin shugaban Kasar, William Ruto.

Babbar mai gabatar da kara a kotun Fatou Bensouda, ta ce akwai shaidar da ke nuna cewa, Walter Barasa ya yi kokarin bada cin hanci ga wani mutumin da yake tsammanin zai bada shaida a kotun, wadda ba za ta yiwa William Ruto dadi ba.

Mista Ruto ya gurfana a gaban kotun ICC, wadda ke tuhumarsa da rura wutar rikicin da ya biyo bayan zabubukan 2007 a Kenya.

Dan jaridar ya shaida wa BBC cewa, a shirye yake ya wanke kansa daga zargin.