Iran ta maida martani ga Isra'ila kan nukiliya

Shugaban kasar Iran, Hassan Rouhani
Image caption Isra'ila ta ce ba za ta yarda Iran ta mallaki makaman nukiliya ba, ko da kuwa in ta kama ta dauki mataki a kai ita kadai

Iran ta mayar da martani mai zafi ga furucin Firai ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu na cewa, sabon shugaban Iran kura ce lullube da fatar akuya.

Da yake jawabi a babban taron Majalisar Dinkin Duniya, Khodadad Seifi na kasar Iran ya ce jawabin Mr. Netanyahu na da kaushi sosai.

Ya jaddada cewa kwata-kwata Iran ba ta da niyyar kera makamin nukiliya, kuma ta amince da dokar hana yaduwar fasahar nukiliya a fadin duniya, yarjejeniyar da har yanzu Isra'ilar ba ta amince da ita ba.

Tun da fari dai Mr. Netanyahu ya ce diplomasiyya ba zai yi aiki ba, har sai an ci gaba da kakabawa Iran takunkumi.