Firai ministan Italiya ya yi nasara a majalisa

Firai ministan, Enrico Letta
Image caption Firai ministan, Enrico Letta

Firai ministan Italiya, Enrico Letta ya sha a kuri'ar yanke kauna ga gwamnatinsa da majalisar dokokin kasar ta kada a birnin Roma.

Mista Letta ya yi nasara ne, bayan da tsohon Firai ministan kasar, Silvio Berlusconi, ya sauya tunani kwatsam.

A da mista Berlusconin ya rantse ne sai ya ga bayan gwamnatin, ta hanyar janye goyon bayan jam'iyyarsa.

To amma tilas ya bada kai bori ya hau, saboda na kurkusa da shi sun yi barazanar za su bijire masa.