Japan ta tallafawa Nijar

Image caption Issoufou Muhammadu, shugaban Niger

Kasar Japan ta taimaka wa ma'aikatar kiwon lafiya ta Jumhuriyar Nijar da wasu kayayyakin kiwon lafiya da kudinsu ya kai dala milyan biyar.

Tallafin, wanda jakadan kasar ta Japan a Nijar, Mista Susumu, ya miƙa wa ministan kiwon lafiya na Nijar din, Malam Mano Agaly.

Nijar za ta yi amfani da shi ne wajen daukar dawainiyar yara masu fama da tamowa.

A baya dai Nijar da sha fama da matsalar karancin abinci.