Majalisa ta yi martani kan taron kasa

Majalisar dokokin Najeriya
Image caption 'Yan majalisar dokokin Najeriyar na da bambancin ra'ayi game da taron tattauna makomar kasar

'Yan majalisun dokokin Najeriya sun tofa albarkacin bakinsu dangane da aniyar shugaban kasar na gudanar da taron tattauna makomar kasar.

'Yan majalisa da dama dai na ganin cewa wannan yunkuri tamkar shisshigi ne a gonarsu.

Jama'a da kungiyoyi a Najeriya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu, game da kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin shata hanyoyi da sharuddan gudanar da wani babban taro na kasa.

Taron da ake sa ran zai duba wasu batutuwan dake haddasa takaddama a kasar da suka shafi rabon kasafin kasa da tsarin shugabancin karba - karba da zamantakewar al'umar kasar da dai sauransu.

Sai dai wani abu da jama'a ke tambaya shi ne menene madafar wannan taro, a halin yanzu ganin cewa Najeriya na bin tsarin demokradiyya mai Shugaban kasa da majalisun dokoki da kuma bangaren shari'a ne, wani abin da tsarin mulkin kasar ya jaddada?