An rufe shafukan intanet a Amurka

Allon dake nuna rufe wajen yawon bude ido na Liberty a Amurka
Image caption An dakatar da shafukan intanet na ma'aikatar gona da na hukumar kidaya ta kasar

Wasu shafukan intanet na gwamnatin Amurka da sakonnin Twitter sun daina aiki, saboda rufe ayyukan wasu hukumomi a kasar.

An rufe shafin hukumar sararin samaniya ta kasar da na fadar gwamnatin Amurka, bayan tsaikon da aka samu a kudaden kashewar gwamnati.

Haka ma shafin intanet na ma'aikatar kula da harkokin tsaro na cikin gida, baya bayar da amsa ga wasikun mutane.

Ita ma ma'aikatar shari'ar kasar, an dakatar da nata shafin intanet.

Tasirin rufe shafukan

Dubban ma'aikata ne suka daina samun sakonninsu na gurin aiki tun a ranar Talata, saboda rufe wasu ma'aikatu da cibiyoyi da kuma hukumomi na kasar.

'Yan kasar na Amurka dai na amfani da shafukan intanet da sakonni Twitter, wajen mika tambayoyi ga cibiyoyin gwamnati.

'Yan majalisa daga bangaren jam'iyyar adawa ta Republican ne suka nuna kin amincewarsu, game da garombawul kan harkokin kiwon lafiya da gwamnatin Obama ke son yi, lamarin da ya kai ga rufe wani bangare na gwamnatin.

Majalisar ta ki amincewa ta sanya hannu a kan dokar da za ta baiwa gwamnati damar kashe kudi a ranar Litinin din da ta wuce.